Mahadi zai bayyana: Kwankwaso zai shiga Kano

Mahadi zai bayyana: Kwankwaso zai shiga Kano

Daya daga cikin jiga-jigan tafiyar kwankwasiyya a jihar Kano, Hajiya Binta Sifikin ta yi magana a kan shigowar Sanata Kwankwaso Kano a karo na farko tun bayan canjin shekar sa daga jam’iyyar APC zuwa tsohuwar jam’iyyar sa ta PDP.

A cewar Hajiya Binta Sifikin, “tabbas Sanata Kwankwaso zai shigo Kano idan lokaci ya yi kuma babu abibda zai iya dakatar da shi.”

A ganawar ta da wakilin jaridar Vanguard, Hajiya Binta Sifikin ta bayyana gamsuwar tad a yadda magoya bayan Kwankwaso ke cigaba da shiga lungu da sako domin wayar da kan jama’a da yada akidar Kwankwasiyyya tare da yin kira gare su da kada su gaza a kan hakan.

Mahadi zai bayyana: Kwankwaso zai shiga Kano
Sanata Rabi'u Kwankwaso
Asali: Getty Images

Zamu jure matsin lamba da tsangwamar da muke fuskanta domin ganin jam’iyyar PDP ta karbi ragamar mulkin jihar Kano da ma Najeriya baki daya,” in ji Hajiya Binta Sifikin.

Kazalika wata shugabar mata a tafiyar Kwankwasiyya, Hajiya Altine Abdullahi, ta bayyana cewar Sanata Kwankwaso na Kano ne kuma jihar Kano tasa ce.

DUBA WANNAN: Jerin sunayen Sanatocin APC 57 da jihohin su

Kwankwaso ne yanzu haka a sahun gaba wajen yiwa gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano adawa, mutumin day a yi masa matimaki lokacin da ya mulki jihar.

Tun a watan Janairu ne hukumar ‘yan sanda a Kano ta shawarci Sanata Kwankwaso ya janye ziyarar da ya shirya kaiwa jihar har sai an samu saukin zazzafan adawar dake tsakanin bangarorin jam’iyyar APC kafin ya fita daga jam’iyyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng