Gwamnatin Kano ta gano wasu mukuden daloli da Kwankwaso ya boye a Ukraine

Gwamnatin Kano ta gano wasu mukuden daloli da Kwankwaso ya boye a Ukraine

Gwamnatin jihar Kano ta gano cewa tsohon gwamnan jihar, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya biya zunzurutun kudi $1,304,618 cikin asusun wata jami'ar dake kasar Ukraine duk da cewa babu dalibin Kano ko guda dake karatu a jami'ar.

Babban mataimaki na musamman a fannin ilimin gaba da sakandare na gwamna Abdullahi Umar Ganduje, Dr Hussaini Akilu Jarma, ne ya yi wannan falasa a ranar Talata yayin kafa kwamitin bayar da tallafin karatu ga daliban jihar Kano.

Jarma yace ya biya jami'ar wannan zunzurutun kudin ne cikin shirinsa na bawa daliban Kano tallafin guraben karo ilimi a kasashen ketare.

Tonon silili: Gwamnatin Kano ta gano wasu mukuden kudade da Kwankwaso ya boye a Ukraine
Tonon silili: Gwamnatin Kano ta gano wasu mukuden kudade da Kwankwaso ya boye a Ukraine

Wata sanarwa data fito daga bakin Abba Anwar, sakataren yadda labarai na gwamna Abdullahi Umar Ganduje, tace "Binciken da aka gudanar ya nuna cewa an saka kudi har $1,304,618 cikin asusun ajiyar wata jami'a a Ukraine a zamanin mulkin gwamna Rabiu Musa Kwankwaso.

DUBA WANNAN: Lalata don bayar da maki: An sake fatatakar wani lakcara a wata jami'ar Najeriya

"Babu wani dalibi da aka aika zuwa jami'ar. An ajiye kudaden ne kawai babu abinda aka aikata dasu. Tabbas dole abubuwa su canja," inji shi.

A jawabinsa, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya gorantawa Kwankwaso kan yadda ya tarawa jihar bashin sama da N4 biliyan da sunnan tallafin kai dalibai karatu kasashen waje duk da yasan cewa lamarin zai ruguje.

"Lokacin da muka karbi mulki, an fada mana cewa tsohuwar gwamnati ta biya dukkan kudaden guraben karo karatun na kasashen waje amma da muka gudanar da bincike sai muka gano hakan ba gaskiya bane," inji Ganduje.

Ganduje ya kokan kan yadda sauran jihohi suka dawo da dalibansu jami'o'in Najeriya saboda tsadar kudin makaranta amma jihar Kano ta cigaba da biya duk da haka wanda hakan ya janyo wa jihar dimbin basusuka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164