Gaba da baya: Naira 7 kacal Muratala ya bari a Duniya lokacin da aka kashe sa

Gaba da baya: Naira 7 kacal Muratala ya bari a Duniya lokacin da aka kashe sa

Shakka babu abin da tsohon Shugaban kasa Janar Murtala Mohammed ya mutu ya bari yana da ban mamaki kwarai da gaske. Kwanan nan binciken mu ya kai mu ga abin da ya faru a wancan lokaci.

Gaba da baya: Naira 7 kacal Muratala ya bari a Duniya lokacin da aka kashe sa

Abiola wanda ya lashe zaben shugaban kasa a 93 yace N7 Murtala ya bari

Wata tsohuwar Jaridar Gaskiya ta fi kobo ta Arewa da aka buga tun a tsakiyar shekarar 1982 ta bayyana abin da aka samu a asusun bankin tsohon Shugaban Kasar Najeriya Marigayi Murtala Ramat Mohammed da aka kashe a 1976.

Naira 7 da kobo 22 kacal ne aka samu a akawun din Murtala Mohammed bayan ya bar Duniya a Ranar 13 ga Watan Fubrairun 1976. Cif MKO Abiola wanda babban Aminin Murtala Mohammed ne shi ya bayyana haka lokacin yana da rai.

KU KARANTA: Wani Gwamnan APC a Kudu ya yi wa Inyamuran Najeriya ta-tas

Marigayi Abiola a lokacin ya bayyana cewa Murtala bai bar wasu dukiyoyi a wasu wurare ba. MKO Abiola wanda ya san Murtala kuma Murtala ya san sa, asali ma dai sun zama kamar wasu ‘Yan uwa ya yaba da halin tsohon Shugaban kasar.

Janar Mohammed ya mulki kasar nan ne na watanni 6 rak a lokacin mulkin Soji, kafin Murtala ya jima a mulki ne wasu su ka kashe sa. Shi ma MKO Abiola wanda ya bada wannan labari ya rasu. Abiola ya rasu ne a gidan yari a lokacin Janar Abacha.

Ku na da masaniyar cewa bayan an kashe Murtala dai, Janar Olusegun Obasanjo ne ya karbi mulkin. Janar Obasanjo ya harbe wadanda suka kashe Janar Murtala Muhammad har lahira. A wancan lokaci Janar Buhari ya rike Gwamna da Minista.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Mailfire view pixel