Wata Mata ta fito takarar Gwamnan Jihar Kaduna a Jam’iyyar APC
Mun samu labari cewa wata Baiwar Allah ta fito takarar Gwamnan Jihar Kaduna a karkashin Jam’iyyar APC mai mulki inda ta ke sa ran doke Gwamna ma-ci Mallam Nasir Ahmad El-Rufai.
Watakila Gwamnan Jihar Kaduna Malam El-Rufai zai fuskanci kalubale a zabe mai zuwa ne har a cikin gida watau Jam’iyyar sa ta APC mai mulki. Hajiya Zainab Ibrahim ce ta sha alwashin tika Gwamnan Jihar da kasa a zaben 2019.
Zainab Ibrahim wanda mu ka ga wasu fastocin ta, ta nuna cewa babu gudu kuma babu ja-da-baya za tayi wannan takara inda ta ke sa ran kada Gwamna mai-ci daga kujerar sa kuma a Jam’iyyar sa. Hakan dai abu ne mai matukar wahala.
KU KARANTA: Ba zan janye shirin takara ta ba ko me zai faru - Dankwambo
Wannan Baiwar Allah da ba tayi fice a siyasa ba tayi karatu ainun inda har ta mallaki Digiri uku watau PhD. Kafin karshen shekarar nan ne za ayi zaben fitar da gwani na Jam’iyyun kasar nan inda za a gwabza babban zabe kuma a cikin 2019.
A Jihar Kaduna dai mun samu labari cewa Uba Sani wanda yana cikin masu ba Gwamna El-Rufai shawara ya fara kokarin tsayawa takarar Sanatan Kaduna ta tsakiya. Kwanan nan Sani ya gana da jama’a a manyan Unguwanni na Yankin Kaduna.
Kwanaki kun ji labari cewa wasu kusoshin Jam’iyyar APC sun fice daga Jam’iyyar a Jihar Kaduna. Jam’iyyar PDP tayi wani babban gangamin da ya rikita APC bayan Sanata Sulaiman Hunkuyi da wasu manyan APC a Jihar Kaduna sun sauya-sheka.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng