Shari'a sabanin hankali: Sun saci kayan dubu 50, an bayar da belin su akan dubu 400

Shari'a sabanin hankali: Sun saci kayan dubu 50, an bayar da belin su akan dubu 400

A ranar Litinin dinnan ne alkalin wata kotun majistire dake jihar Sokoto, ya bayar da belin wasu kananan 'yan kasuwa guda hudu akan kudi naira 400,000

Shari'a sabanin hankali: Sun saci kayan dubu 50, an bayar da belin su akan dubu 400
Shari'a sabanin hankali: Sun saci kayan dubu 50, an bayar da belin su akan dubu 400

A ranar Litinin dinnan ne alkalin wata kotun majistire dake jihar Sokoto, ya bayar da belin wasu kananan 'yan kasuwa guda hudu akan kudi naira 400,000, wadanda ake zargin su da sata da kuma kokarin cinye hakkin wani.

Wadanda ake zargin sun hada da; Bashar Malami, mai shekaru 28; Hassan Umar, mai shekaru 27; Mubarak Hassan, mai shekaru 26 sai kuma Saifullahi Mohammed, mai shekaru 26.

DUBA WANNAN: Shaidan ya shiga tsakanin Trump da matarsa Melania

Wadanda ake tuhumar, wanda suke zaune a cikin garin Sokoto, suna fuskantar hukuncin kotu, akan hada baki wurin aikata ta'addanci, sata da kuma kwace.

Alkalin kotun majistiren, Abubakar Adamu, wanda ya bayar da belin masu laifin akan kudi naira 100,000 kowannen su, ya kuma bukaci su gabatar da shaidu, wadanda zasu tsaya musu. Alkalin ya bukaci shaidun su zamanto suna cikin kotun. A karshe alkalin ya daga karar wadanda ake zargin zuwa ranar 15 ga wannan watan.

Dan sandan da ya gabatar da masu laifin, Insp Khalid Musa, ya bayyana wa kotu cewar wadanda ake tuhumar sun aikata laifin nasu a ranar 17 ga watan Yuli shekarar 2017 a garin Sokoto.

Musa ya bayyana cewa wadanda ake tuhumar sun shiga gidan wani mutumi mai suna Bello Shehu, wanda yake zaune a unguwar Minanata, inda suka kwashe yashi tifa daya da kuma bulo na siminti guda 180, wanda kudin su ya kai naira 51,600.

Dan sandan ya kara da cewa wadanda ake tuhumar sun sayarwa da wani mutumi mai suna Hassan Umar akan kudi naira 10,500, inda aka samu kudi naira 2,500 a wurin shi lokacin da ake gabatar da bincike akan shi.

Alkalin ya ce laifin nasu ya sabawa sashi na 97,317 da kuma sashi na 287 na dokar kasa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng