Talata ne: Sarkin Musulmi ya sanar da ranar Idi

Talata ne: Sarkin Musulmi ya sanar da ranar Idi

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar ya sanar da ranar Lahadi, 12 ga watan Agusta a matsayin ranar farko na sabuwar watar Zulhajji, ma’ana jiya Lahadi, ya zama 1 ga watan Zulhajji kenan.

Legit.ng ta ruwaito mataimakin sakataren kwamitin kula da al’amuran Musulunci, Farfesa Salisu Shehu ne ya sanar da haka a ranar Lahadi 12 ga watan Agusta a madadin Sarkin Musulmi, inda yace bayan doguwar tattaunawa ce aka samar da wannan rana.

KU KARANTA: Malaman Arewa sun shirya yadda za su kawo karshen shi'a

“Mun tabbatar da farkon watan Zulhijja ne bayan tattaunawa da kwamitin fatawa, wanda ta bayyana cewar ana tsayar da watan Zulhijja ne ta hanyar duba da watan kasar Saudi Arabia, da wannan ne mai alfarma Sarkin Musulmi ya sanar da Lahadi, 12 ga watan Agusta a matsayin ranar 1 ga watan Zulhijja.” Inji shi.

Salisu ya cigaba da cewa ana bukatar al’umma Musulmai dasu yi ma kasa Najeriya addu’a, da mahajjata, haka zalika ana kira ga Musulmai da su ci moriyar kwanaki goma na watan Zulhijja, musamman Azumin ranar Arafa, da zai kama a ranar Litinin 20 ga watan Agusta.

Daga karshe mai alfarma Sarkin Musulmi ya sanar dsa ranar Talata, 21 ga watan Agusta a matsayin ranar babbar Sallah na shekarar 1439 bayan Hijira.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel