Sultan ya aike da sako ga sako na musamman ga musulmi a kan watan Dhul Hijjah

Sultan ya aike da sako ga sako na musamman ga musulmi a kan watan Dhul Hijjah

Mai alfarma sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar, ya nemi musulmi da su fara duba sabon watan Dhul Hijjah daga yau, Lahadi, 12 ga watan Agusta.

Sarkin Musulmin ya bayar da wannan umarni ne a cikin wani sako da Farfesa Sambo Junaidu, shugaban kwamitin bayar da shawara a kan harkokin addini, ya saka wa hannu yau a Sokoto.

Sultan ya aike da sako ga sako na musamman ga musulmi a kan watan Dhul Hijjah
Sarkin Muslmi

"Muna sanar da al'ummar musulmi da su fara duba sabon watan Dhul Hijjah daga yau Lahadi 12 ga watan Agusta wacce tayi daidai da ranar 29 ga watan Dhul Qadah," a cewar sanarwar.

DUBA WANNAN: Aisha Buhari ta isa kasar Koriya domin karbo digirin girmamawa, hotuna

"Musulumi su fara duba watan domin sanarwa dagatai ko hakimai dake kusa da su domin isar da sako ga mai alfarma sarkin Musulmi," sanarwar ta kara da fadi.

Kazalika ya yi addu'a ga Allah da ya bawa musulmi ikon yin aiyuka na alheri.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng