Tsohon shugaban jam'iyyar PDP da dubban magoya bayansa sun koma APC
Tsohon shugaban jam'iyyar PDP a jihar Sokoto, Alhaji Abubakar Shehu Tambuwal, ya koma jam'iyyar APC tare magoya bayansa a kalla 10,000.
Da yake jawabi ga dumbin jama'a a yau, Lahadi, yayin taron bikin komawar sa APC, Shehu Tambuwal, ya bayyana cewar sun yanke shawarar komawa jam'iyyar ne saboda irin yadda take tafiyar da al'amuran gwamnati cikin gaskiya da rikon amana.
Ya kara da cewar sun yanke wannan shawara ne bisa ra'ayin kansu bayan nazarin yadda gwamnatin APC ke jagorantar ragamar mulkin Najeriya.
DUBA WANNAN: Abin kunya: Kyauta Obasanjo yake bawa mata rijiyar man fetur bayan yin lalata da su – Farfesa Soyinka
Shehu Tambuwal tsohon kwamishina ne na ilimi a jihar ta Sokoto.
Yayin gabatar da jawabinsa, shugaban jam'iyyar APC a karamar hukumar Tambuwal, Alhaji Umar Maitafsiri, ya bayyana cewar tsohon shugaban jam'iyyar ta PDP ya canja shekar ne tare da magoya bayansa fiye da 10,000 da suka fito daga kananan hukumomin Yabo, Kebbi, Tureta, Dange/Shuni, Bodinga da Shagari.
Da yake mika katin shaidar zama dan APC ga Shehu Tambuwal, shugaban jam'iyyar na jihar Sokoto, Alhaji Sadik Achida, ya tabbatarwa da wadanda suka canja shekar cewar ba za a nuna masu wariya ko banbanci ba.
Kazalika ya bayyana cewar gwamnatin shugaba Buhari zata cigaba da warware matsalolin da suka dade suna damun Najeriya musamman ta fuskar aiyukan raya da cigaban al'umma a kowanne mataki.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng