Idan na samu mulki wa’adi guda kurum zan yi – Inji Atiku Abubakar

Idan na samu mulki wa’adi guda kurum zan yi – Inji Atiku Abubakar

-Alhaji Atiku Abubakar yace ba zai yi wa’adi fiye da guda a mulki ba

-Tsohon Mataimakin Shugaban kasar yace ba zai yi alkawari ya saba ba

-‘Dan takarar yace Buhari yayi wa al’umma alkawari ya gaza cikawa

Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayyana cewa idan aka zabe sa Shugaban kasa ba zai yi irin na Buhari ba. Alhaji Atiku Abubakar yace idan ya samu mulki ba zai nemi tazarce ba.

Idan na samu mulki wa’adi guda zan yi – Inji Atiku Abubakar
Ba zan yi irin na Buhari ba idan aka zabe ni - Atiku

Atiku Abubakar yace idan aka zabe sa a karkashin Jam’iyyar PDP ba zai nemi ya zarce a kan kujera ba. Tsohon Mataimakin Shugaban na Najeriya ya bayyana wannan ne lokacin da yayu wata doguwar hira da Jaridar nan ta This Day.

KU KARANTA: PDP ta tika APC da kasa a wajen wani zaben 'Dan Majalisa

Atiku yace shi ba zai yi irin na Shugaba Muhammadu Buhari ba idan har aka mika masa ragamar mulkin kasar nan. Atiku wanda yake neman mulkin kasar nan yace shekara 4 kacal zai yi a ofis ba tare da ya nemi zarcewa a mulki ba.

‘Dan takarar Shugaban kasar na PDP yace idan ta kama za a iya yarjejeniya da shi a rubuce domin a gwangwaje cewa ba zai mulki Najeriya sau biyu ba. Atiku yace Shugaba Buhari yayi irin wannan alkawari a 2011 amma ya saba.

Tsohon Mataimakin Shugaban kasar a lokacin Obasanjo yace babu wanda ya tursasa sa wajen daukar wannan mataki. Atiku yace ba zai yaudari jama’a ba domin shi ba irin Buhari bane wanda ya rika yin alkawuran da ya gaza cikawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng