Barawo ya yanka wata dalibar jami'ar Bayero ta Kano a dakin kwanan dalibai mata
A daren ranar Alhamis ne wani barawo, da ya zuwa yanzu ba a gano ko waye ba, ya yanki wata dalibar jami'ar Bayero da wuka a wuya a dakin kwanan dalibai mata dake sabon ginin jami'ar.
Barawon ya aikata wannan ta'addanci ga dalibar ne da misalin karfe 3:00 na dare lokacin da take kokarin shiga daki bayan ta dawo daga karatun dare.
Barawon ya kwace mata waya da wasu kayan dake jakarta ta hannu.
Daya daga cikin daliban jami'ar ta bayyana cewar dalibar tayi ihun neman taimako amma sai dai lokacin da suka iso inda take tuni barawon ya tsere.
"Mun gaggauta kai ta asibiti inda aka kwantar da ita domin ceto rayuwar ta," a cewar dalibar.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Shamsudden Umar, shugaban kula da harkokin dalibai na jami'ar ya bayyana cewar dalibar na samun kulawa da sauki a asibitin.
DUBA WANNAN: Rashin imani:
Umar ya kara da cewa tuni shugaban jami'ar, Farfesa Yahuza Bello, ya bayar da umarnin fara bincike a kan lamarin tare da bayar da wani umarni na kara tsayin katangar dakin da ta kewaye muhallin dalibai mata da kuma saka fitulu ko ina.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng