Kallabi tsakanin rawwuna: Yan Matan Najeriya sun yi zarra a gasar kimiyya da fasaha ta Duniya

Kallabi tsakanin rawwuna: Yan Matan Najeriya sun yi zarra a gasar kimiyya da fasaha ta Duniya

Ayarin yan Najeriya da suka wakilci kasar a gasar fasahar kirkira daya gudana a kasar Amurka, wanda ta kunshi yan mata daliban Sakandari sun yi zarra a gasar, inda suka lashe babbar kyautar da aka sanya.

Mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ne ya sanar da haka a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Facebook, inda ya yaba ma yan matan, tare da jinjina ma kwazon da suka nuna wajen fitar da Najeriya daga kunya, tare da baiwa marada kunya.

KU KARANTA: Likafa ta ci gaba: Shugaban majalisar dinkin Duniya ya nada Amaechi babban mukami

Kallabi tsakanin rawwuna: Yan Matan Najeriya sun yi zarra a gasar kimiyya da fasaha ta Duniya
Yan Mata

Yan matan da suka wakilci Najeriya a wannan gasar ta Duniya mai taken ‘2018 Technovation World Pitch’ da aka yi shi a jihar California na kasar Amurka sun kirkiri wani manhaja ne da zai iya gane ingancin magani ko akasin haka, da suka rada ma suna ‘FD Detector’.

Yan matan sun ciri tuta ne a tsakanin dalibai dubu goma sha tara (19,000) da suka fito daga kasashen Duniya dari da goma sha biyar, inda Najeriya ta fafata kasashe biyar a zagaye na karshe, da suka hada da China, Spain, Turkey, United States, da Uzbekistan, kuma ta yi nasara.

Kallabi tsakanin rawwuna: Yan Matan Najeriya sun yi zarra a gasar kimiyya da fasaha ta Duniya
Kyautar zinari da suka samu

Legit.ng ta ruwaito Osinbajo ya jinjina ma wata mata mai suna Uchenna Onwuamaegba-Ugwu shugaban cibiyar kimiyya da fasaha na Technik STEM Center da ta horas da yan matan su biyar.

Daga karshe Osinbajo yace daliban sun zama abin alfahari ga Najeriya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel