Zaben 2019: Daga Daura sai Madobi Inji Sanata Rabiu Kwankwaso

Zaben 2019: Daga Daura sai Madobi Inji Sanata Rabiu Kwankwaso

Mun samu labari cewa Tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya caccaki Magajin sa watau Abdullahi Umar Ganduje a wajen taron yakin neman zaben PDP da aka yi jiya a Katsina inda ya kuma yi kira a zabi PDP a 2019.

Zaben 2019: Daga Daura sai Madobi Inji Sanata Rabiu Kwankwaso
Sanata Rabiu Kwankwaso wajen kamfen din PDP a Katsina

A wajen kamfen din PDP da aka yi a Garin Kankiya da ke cikin Jihar Katsina jiya Alhamis, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso wanda yanzu ya bar Jam’iyyar APC ya caccaki Gwamnan na Kano mai-ci Ganduje ko da dai bai ambaci sunan sa ba.

Sanata Kwankwaso ya fadawa mutanen Kano cewa su gaida Mijin Hajiya idan sun koma gida sannan daga karshe yace yana gaida ita ma Hajiyar. Ba mamaki dai sakon Kwankwaso shagube ne ga tsohon Mataimakin sa Mai Girma Ganduje da Mai dakin sa.

KU KARANTA:

Jam’iyyar PDP mai adawa dai ta shirya gagarumar kamfe ne a Garin Kankiya inda ake shirin zaben ‘Dan Majalisar Dattawa na Yankin Daura bayan rasuwar Sanatan Yankin kwanakin baya. Kwankwaso a wajen taron yace daga Daura sai Madobi.

Ma’anar daga Daura sai Madobi dai shi ne Kwankwaso zai canji Buhari a zaben 2019. A wajen kamfen din Kwankwaso yayi wa Katsinawa ta’azziyar rashin manyan Malamai da Dattawa da su kayi tare da jajen musibar ruwa da aka gani.

Bisa dukkan alamu dai Sanatan zai nemi takarar Shugaban kasa a 2019 inda yayi kira ga mutane sun fita su yi zabe a 2019 domin ceto al’umma daga wahalar da ake ciki. Dama kun ji labari cewa Hadiman Ganduje da dama sun yi murabus a baya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng