Madalla: Saudiyya ta kirkiro wata manhajar tantance wa'azi
- Kasar Saudiyya ce kanwa uwar-gami kan yada zafafan akidu da suka haifar da zafin ra'ayi a tsakanin samari a shekarun baya
- Yariman kasar Saudiyya mai jiran gado, ya sha alwashin sauya hakan, musamman bayan da shugaban Amurka ya kai ziyara kasar a bara
- Manhajar zata baiwa gwamnati damar sanya ido, kan masu wa'azi, za kuma ta baiwa masu jin wa'azin damar tantance tsawo ko kaucewar wa'azin daga turba
Hukumomi a Saudiyya na kirkirar wata manhajar wayar hannu wacce za ta sa ido kan wa'azuzzuka da addu'o'i a masallatai domin bai wa masu ibada damar sani idan mai wa'azi zai dade yana wa'azin.
Jaridar Al-Watan ta kasar Saudiyya ta ruwaito cewa Ministan harkokin musulunci na kasar Abdul Latif Al-Sheikh, ya bayyana cewa manhajar za ta bayar da damar sa ido a masallatai, kan tsawon lokaci da kuma ingancin wa'azuzzukan duk minti kuma duk dakika.
A baya dai, kasar Saudiyya, ta bar Maluma su ci karensu babu babbaka kan wa'azozi da maqaloli wadanda tuni suna kai wasu ga zama 'yan ta'adda, duk domin kokarin kautar da jama'a daga bin kasar Iran mai yada shi'anci.
DUBA WANNAN: Gwamnatin Najeriya ta kasa jure wa adawa
Yanzu kam, kungiyoyi da yawa masu irin wannan zafin ra'ayi, kamar ta Muslim Brotherhood da Misra, tuni an haramta ta a matsayin ta 'yan ta'adda, duk don gyara kura-kuran baya.
Ko a Najeriya ma, an sami bullar irin wadannan masu zafin ra'ayi, wadanda suka haramta boko suke kuma kokarin kafa daular Islama, watau Boko Haram.
A halin da a ke ciki, Saudiyya na duba batun kawo sauyi a koyarwar addini, kuma a na ci gaba da muhawara kan daidaita abubuwan da a ke wa'azi a kan su domin karakatar da mutane daga ra'ayin kasashen waje, ko na bangaranci ko kuma na kungiyar 'yan uwa musulmi.
Ministan ya ce addini "ba fagen da za a rikita zukatan mutane ba ne, ko kuma a yi sagegeduwa da tsaro da zaman lafiyar kasar nan mai albarka ba".
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng