Sani Sidi ya mika takardar tsayawa takarar gwamna a jihar Kaduna

Sani Sidi ya mika takardar tsayawa takarar gwamna a jihar Kaduna

Tsohon shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta Kasa wato NEMA, Sani Sidi ya mika takardar tsayawa takarar gwamna a jihar Kaduna.

Sani Sidi ya mika takardar ne a ofishin Jam’iyyar PDP dake Kaduna.

A jawabin sa Sidi ya bayyana cewa ya takarar kujerar ne saboda ya dawo da martabar jihar da aka santa da shi.

Sani Sidi ya mika takardar tsayawa takarar gwamna a jihar Kaduna
Sani Sidi ya mika takardar tsayawa takarar gwamna a jihar Kaduna

Ya ce: “Na zo wannan ofishi ne domin in mika takardar muradin yin takarar gwamnan jihar Kaduna a Inuwar Jam’iyyar PDP. Na yanke wannnan shawara ne domin nuna godiya ta ga jama’ar jihar Kaduna game da irin gudunmuwar da suka bani a tsawon ayyukan da nayi a rayuwa ta.

KU KARANTA KUMA: Kalli yadda aka yiwa Saraki bayan ya shiga majalisa (bidiyo)

“Lokaci yayi da zan saka wa mutanen jihar Kaduna bisa ga abin da suka yi mini. Babban haryar da naga ya fi dacewa kuwa shine ta wannan hanya.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng