Aikin bada tallafin N5000 ga gajiyayyu ya kankama a jihar Jigawa (Hotuna)

Aikin bada tallafin N5000 ga gajiyayyu ya kankama a jihar Jigawa (Hotuna)

A fada a cika, Hausawa suka ce said an Kunya, wannan shine gaskiyar abinda ya faru a jihar Jigawa, inda jami’an gwamnati suka isa jihar Jigawa suna cigaba da daukan bayanai daga mutanen da aka zaba don amfana da wannan kudi.

Shafin jaridar ‘Najeriyarmu a yau ce’ ta bayyana haka a shafinta na Facebook, inda aka hangi jami’an gwamnati suna daukan hotunan wasu tsofaffi, daga cikin wadanda zasu ci moriyar wannan tallafi.

KU KARANTA: Zan hukunta duk wadanda suka shirya ma Majalisa manakisa – Inji Mukaddashin shugaban kasa

Aikin bada tallafin N5000 ga gajiyayyu ya kankama a jihar Jigawa (Hotuna)
Aikin bada tallafin N5000

Legit.ng ta ruwaito tun a yayin gudanar da yakin neman zabe na shekarar 2015 ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin biyan Naira dubu biyar biyar ga yan Najeriya gajiyayyu da wadanda ke cikin matsananciyar bukata.

Daga cikin irin wannan ayyukan tallafi da gwamnatin Buhari ta alkawranta akwai samar ma matasa dubu dari biyar aiki a karkashin tsarin N-Power, shima wannan alkawari an kammala cika shi, haka zalika akwai batun ciyar da dalibai abinci, inda a yanzu haka gwamnati na ciyar da daliban 1 zuwa 3 na makarantun Firamari a jihohi goma sha tara.

Aikin bada tallafin N5000 ga gajiyayyu ya kankama a jihar Jigawa (Hotuna)
Aikin bada tallafin N5000

Zuwa yanzu akalla mutane dubu dari hudu, 400,000 ne ke amfana da tallafin naira dubu biyar biyar a jihohi Ashirin na Najeriya, yayin da gwamnatin ke dakon sauran jihohi su kammala shirye shiryen da ake bukata dage garesu kafin su fara amfana.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng