Yanzu Yanzu: Jami’an DSS sun mamaye harabar majalisar dokokin kasar (bidiyo)
Jami’an hukumar DSS sun mamaye majalisar dokokin kasar a yayinda ake yunkurin sake bude zangon majalisar ga yan majalisa masu biyayya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Babban sakataren labarai na majalisar dattawa, Sanni Onogu ya tura sako ga manema labarai dake daukar rahoton majalisar dokokin kasar a daren jiya kan cewa su zama a shirye domin ana iya bude majalisar a yau.
Sai dai wasu yan jarida da suka isa zangon a safiyar yau Talata, 7 ga watan Agusta basu samu shiga ba sakamakon mamaye zangon da jami’an DSS suka yi.
Haka kuma an hana jami’an shiga zangon. Babuwani bayani da aka ba manema labarai wadda suka tursasa don son sanin dalilin hana su shiga zangon.
KU KARANTA KUMA: Gwamna Bindow ya nada sababbin Kwamishinoni 2 a Gwamnatin sa
An tattaro cewa jami’an tsaro sun fara mamaye wajen ne da misalin karfe 4:00 na asuba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng