Kaico! Wata Mota dauke da maniyyata aikin Hajji ta tunjuma cikin Rafi a jihar Katsina

Kaico! Wata Mota dauke da maniyyata aikin Hajji ta tunjuma cikin Rafi a jihar Katsina

Allah ya takaita wani mummunan hatsari da ya faru a jihar Katsina, inda wasu matafiya, kuma maniyyata aikin Hajjin bana suka tunjuma cikin wani Rafi dake gefen hanya, kamar yadda Legit.ng ta samu rahoto.

Wani ma’abocin kafar sadarwar zamani, Husaini Iliyasu Chiranci ne ya bayyana wannan labari a shafinsa na Facebook, inda yace maniyyatan sun fito ne da nufin isa filin sauka da tashin jirage na jihar Katsina don wucewa kasa mai tsarki.

KU KARANTA: Dakarun Sojojin Najeriya sun ragargaji yan bindigar jihar Benuwe

Kaico! Wata Mota dauke da maniyyata aikin Hajji ta tunjuma cikin Rafi a jihar Katsina
Motar

Sai dai kash, a yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Katsina, lokacin da suka kai garin Charanchi, dake karamar hukumar Charanchi ne wani mai babur ya gitta ma Motarsa tasu, inda a garin kauce ma dan babur din suka afka cikin wani Rafi.

Nan da nan jama’a suka shiga kokarin ceto maniyyatar, aka kuma ci sa’a wajen dukkan maniyyatan, sai dai babu tabbacin ko tafiyartasu na nan ko kuwa za’a daga shi.

Kaico! Wata Mota dauke da maniyyata aikin Hajji ta tunjuma cikin Rafi a jihar Katsina
Maniyyata

A wani labarin kuma, a ranar Litinin, 6 ga watan Agusta ne jerin mahajjata na farko daga jihar Katsina guda 560 suka isa birnin Madinah a kasar Saudiyya a shirye shiryen gabatar da aikin Hajji.

Kaakakin hukumar Alhazai ta jihar Katsina, Badaru Bello ne ya sanar da haka, inda yace mahajjatan sun fito ne daga Bakori, Danja, Dandume, Faskari, Funtua da karamar hukumar Sabuwa, mahajjatan sun hada da Maza 366, Mata 188 sai wasu Maza shida daga jihar Jigawa.

Kaico! Wata Mota dauke da maniyyata aikin Hajji ta tunjuma cikin Rafi a jihar Katsina
Maniyyata

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng