Zakaran gwajin dafi: Dalibi daga Arewacin Najeriya ya yi zarra a jarabawar JAMB
Hukumar gudanar da jarabawar shiga makarantun gaba da sakandari, JAMB, ta sanar da dalibin da yafi samu sakamako mai kyawu da adadin maki mafi yawa a jarabar JAMB ta shekarar 2018, inda wani dalibi daga yankin Arewa ya samu wannan kambu.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito JAMB ta bayyana dalibi mai suna Israel Zakari dan asalin karamar hukumar Biu ta jihar Borno a matsayin zakakurin JAMB na shekarar 2018, bayan ya samu maki 364 a jarabawar.
KU KARANTA: Yadda wani Mutumi ya kashe masoyiyarsa sakamakon gano kwaroron roba a Jakarta
JAMB ya bayyana cewa Zakari ya zana jarabawar ne a jihar Ogun, kima ya sha gaban Adekunle Jesufemi daga jihar ogun wanda ya samu maki 358, Alikah Oseghhale daga jihar Edo da ta samu 357 da Ademola Adetola daga jihar Ogun mai maki 355.
Yayin da aka samu dalibai Uku da suka na biyar, Akinyemi Paul daga Ogun, Terhemba Moses daga Benuwe da Obi Obouha Abiamamela daga Fatakwal da suka samu maki 354.
Daraktan watsa labaru na hukumar, Fabian Benjamin ne ya bayyana sunayen daliban nan a ranar Lahadi,5 ga watan Agusta, inda ya yi kira ga kungiyoyi da marubuta masu bukatar yin rubuce rubuce akan JAMB da su nemi sahihan bayanai daga hukumar.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng