Haduwar Kwankwaso da Shekarau: Ta ciki na ciki – Inji jam’iyyar APC

Haduwar Kwankwaso da Shekarau: Ta ciki na ciki – Inji jam’iyyar APC

Uwar jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta bayyana haduwar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Malam Ibrahim Shekarau a matsayin haduwar da ban a Allah da Annabi bane, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Mataimakin shugaban APC na Kano, Shehu Maigari ne ya bayyana haka a ranar Lahadi, 5 ga watan Agusta, inda yace haduwar tsofaffin gwamnonin jihar biyu ba zai rage ma APC komai ba a zaben 2019, aka ce ko a jikina, wai an tsikari kakkausa.

KU KARANTA: Masu garkuwa sun saki Sheikh Al-Garkawy bayan karbar miliyoyin kudin fansa

Ya kara da cewa nan bada jimawa ba za’a gansu a rana, domin kuwa a tarihinsu basu taba zama a inuwa day aba, sakamakon suna da akidunsu na siyasa ya bambanta sosai: “Siyasa lamari ne na akida guda, amma Kwankwaso da Shekarau basu da akida daya, kuma hanyar kare daban hanyar mota daban.

Haduwar Kwankwaso da Shekarau: Ta ciki na ciki – Inji jam’iyyar APC

Haduwar Kwankwaso da Shekarau

“Don haka ba zasu iya zama tare su yi aiki tare ba, don haka jama’a sun zura idanu don ganin yaddda zata kaya a tsakaninsu, Kwankwaso ne zai yi rinjaye ko kuwa Shekarau.” Inji shi.

Daga karshe Maigari ya bayyana cewa ta tabbata a yanzu cewa Kwankwaso da Shekarau ba bukatar jama’a suka sanya a gaba ba, bukatar kansu ta kashin kai ne kawai damuwarsu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel