Wadanda suka sauya sheƙa sai sun yi nadama, 'Yan Najeriya na tare da APC - Wamakko

Wadanda suka sauya sheƙa sai sun yi nadama, 'Yan Najeriya na tare da APC - Wamakko

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya bayyana cewa, tabbas dukkanin wadanda suka sauya sheƙa daga jam'iyyar APC zuwa PDP sai sun yi nadamar abinda suka aikata.

A ranar Asabar din da ta gabata ne Wamakko ya bayyana hakan yayin da magoya baya suka gudanar da gangami na tattaki domin bayyana soyayyar su ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam'iyyar sa ta APC a jihar Sakkwato.

Rahotanni sun bayyana cewa, jihar ta Sakkwato ta tumbatsa a ranar da ta gabata yayin da Wamakko ya sauka a mahaifar sa domin tabbatar wa da gwamnan jihar, Aminu Waziri Tambuwal soyayyar Buhari da APC dake zukatan al'ummar jihar.

Wadanda suka sauya sheƙa sai sun yi nadama, 'Yan Najeriya na tare da APC - Wamakko
Wadanda suka sauya sheƙa sai sun yi nadama, 'Yan Najeriya na tare da APC - Wamakko

Legit.ng ta fahimci, Gwamna Tambuwal a ranar 1 ga watan Agusta da ta gabata ya sauya sheƙa daga jam'iyyar sa ta APC zuwa jam'iyyar adawa ta PDP.

KARANTA KUMA: Hukumar Sojin Sama ta tarwatsa wata Maboyar 'Yan Boko Haram a Jihar Borno

Sanata Wamakko yayin mayar da martanida nunawa Tambuwal iyakar sa ya bayyana cewa, jam'iyyar APC reshen jihar Sakkwato na da Sanatoci 2, 'yan Majalisar wakilai 7 da kuma na dokoki ta jiha 12. Baya ga yawan adadin na jiga-jigan dattawa 'yan siyasa, matasa da mata.

A nasa jawaban, shugaban jam'iyyar APC reshen jihar Sakkwato Alhaji Sadiq Achida, ya bayyana cewa har yanzu jihar na goyon bayan shugaba Buhari wanda wannan tumbatsa da jihar ta yi a halin zai sanya nadama cikin zukatan wadanda suka sauya sheƙa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel