Anyi walkiya mun gansu: Shugaba Buhari yace yanzu lokaci ne da Allah yake ware baragurbi daga jam'iyyar APC
- Shugaba Buhari yace wa yan jam'iyyar sa ta APC kada su damu da ficewar da wasu daga cikin jam'iyyar suke yi
- Yayi kira ga yan Bauchi dasu bawa Gumau kuri'un su
Shugaban kasa Muhammad Buhari yace wa yan jam'iyyar sa ta APC kada su damu da ficewar da wasu daga cikin jam'iyar suke, inda yace "da sannu Allah zai fitar da bara gurbi daga cikin mu".
Mai bawa Shugaban kasar shawara a fannin labarai Mr Femi Adesina yayin da yake magana a Abuja yace Shugaban ya bada wannan shawara ne a yayin gudanar da kamfen a jihar Bauchi a ranar Alhamis dinnan data gabata.
DUBA WANNAN: Sa'a tafi manyan kaya: Ahmed Musa ya koma Saudiyya da murza leda
Anyi gangamin ne don goyawa Alhaji Lawan Gumau baya inda ya tsaya takarar Sanata a Bauchi a zaben dazai gudana a ranar 11 ga watan Augustan nan.
Buhari ya tabbatar wa magoya bayan APC cewa gwamnatin zataci gaba da aiki tukuru don cika alkawarin da suka dauka a yayin yakin neman zabe.
"Munayin aiki ne saboda Allah, saboda kasar mu da kuma al'umma, inason sanar daku cewa darasin da muka samu a cikin shekarun nan bazamu taba bari aci amanar ku ba".
"Kamar yanda mukayi alkawarin kawo cigaba a kasar mu ta hanyar tsaro da kuma dakatar da cin hanci da rashawa.
"Munyi kamfe akan haka sannan an zabemu saboda hakan kuma bazamu taba mantawa ba, ya bayyana wa dinbin magoya baya a fili wasa na Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi.
Shugaban yayi kira ga jama'ar Bauchin dasu bawa Gumau goyan baya a zaben da zai gudana.
Ya kara da mika godiya ga mutanen yanda suka fito cikin ruwa domin yi masa maraba sannan da nuna goyan bayansu ga jam'iyyar dangane da zaben da za'a gudanar.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng