Masu canja sheka: Osinbajo sunyi wata ganawa da Akpabio a Villa

Masu canja sheka: Osinbajo sunyi wata ganawa da Akpabio a Villa

A jiya ne mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya gana da shugaban marasa rinjaye na majalisa, Sanata Godswill Akpabio dangane da mahukuntan da suka bar jam'iyyar PDP zuwa APC

Masu canja sheka: Osinbajo sunyi wata ganawa da Akpabio a Villa
Masu canja sheka: Osinbajo sunyi wata ganawa da Akpabio a Villa

A jiya ne mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya gana da shugaban marasa rinjaye na majalisa, Sanata Godswill Akpabio dangane da mahukuntan da suka bar jam'iyyar PDP zuwa APC.

Tsohon gwamnan Akwa Ibom ya samu zuwa gidan gwamnatin jihar da misalin 3:06 na yamma tare mataimakin shugaban kasa akan al'amuran majalisar dattawa, Sanata Ita Enang.

DUBA WANNAN: Kalli yawan kuri'un da ake saran Buhari zai samu a Kudancin Najeriya

Taron da ya kai su har karfe 5:20 na yamma yazo karshe ne da zancen shirin barin jam'iyya da Akpabio yake yi. Akpabio na yunkurin barin jam'iyyar ne saboda rashin shirin dake tsakanin shi da gwamnan jihar Akwa Ibom Udom Emmanuel.

Majiyar mu tace a lokacin da Akpabio ke tare da mataimakin shugaban kasar, ana taron zababbun jam'iyyar shi ta PDP tare da Bukola Saraki da sauran wadanda suka bar jam'iyyar APC.

Wani Sanata ya sanar da majiyar mu cewa, tuni Akpabio ya gama shirye shiryen barin jam'iyyar PDP.

"Ba don hana shi da Saraki yayi ba, da a ranar talata Akpabio zai sanar da barin jam'iyyar PDP " inji sanatan da ya bukaci a boye sunan shi.

Idan Akpabio ya bar PDP, zai zamo Sanata na biyu daga jihar Akwa Ibom mai arzikin man fetur da ya koma APC, bayan da Sanata Nelson Effiong ya koma APC.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng