Rikicin Shehu Sani da El-Rufai ya barka Jam’iyyar APC a Kaduna

Rikicin Shehu Sani da El-Rufai ya barka Jam’iyyar APC a Kaduna

- Jam’iyyar APC ta dakatar da Sanatan Kaduna Shehu Sani

- APC ta zargi Sani da sukar Gwamnatin Buhari da El-Rufai

- Shugaban Jam’iyya yace ba a dakatar da ‘Dan Majalisar ba

Rikicin Shehu Sani da El-Rufai ya barka Jam’iyyar APC a Kaduna
Jam’iyyar APC a Kaduna ta shiga rikici kan batun Shehu Sani
Asali: UGC

Mun samu labari cewa rikicin da ke tsakanin Sanatan Kaduna Shehu Sani da kuma Gwamnan Jihar Mai girma Malam Nasir El-Rufai ya kara kunno kai inda har ta kai Jam’iyya ta jadadda cewa an dakatar da Sanatan daga APC.

Shugaban Jam’iyyar APC na Mazabar ‘Dan Majalisar da ke Tudun Wada watau Ibrahim Salisu Togo ya tabbatar da cewa an dakatar da Sanatan daga Jam’iyya. Jam’iyyar kuma tace har yanzu ba a janye wannan matakin ba.

KU KARANTA: Ba za a taba samun irin Shugaba Buhari ba a Najeriya inji wani ‘Dan fim

Sai dai shi kuma Shugaban APC na Jihar Kaduna Emmanuel Jakada ya bayyanawa manema labarai cewa an saba doka wajen dakatar da Sanatan. Shugaban na APC yace ya sa kwamitin domin a duba lamarin a kuma yi sulhu.

Shugabannin Jam’iyyar APC da ke karamar Hukumar Kaduna ta Kudu sun dakatar da ‘Dan Majalisar har sai baba ta gani saboda sukar Gwamnatin Nasir El-Rufai da kuma Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da yake yi.

Sabon Shugaban APC na Jihar Kaduna Jakada ya tabbatar da cewa bai san da batun dakatar da ‘Dan Majalisar daga Jam’iyya ba. Shi dai Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai yace dole sai Sanatan ya ba al’ummar Kaduna hakuri.

Kun san cewa Uwar Jam’iyyar APC mai mulki ta nada Yekini Nabena wanda shi ne Mataimakin Sakataren yada labarai na Jam’iyyar ya maye gurbin da Bolaji Abdullahi ya bar matsayin sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng