Tambuwal abin tausayi ne yanzu - Wamakko
Sanata Wamakko ya sanarwa da manema labarai cewa yana na a matsayin dan jam'iyyar APC, babu gudu, ba ja da baya
Sanata Wamakko ya sanarwa da manema labarai cewa yana na a matsayin dan jam'iyyar APC, babu gudu, ba ja da baya. Sannan kuma "Mutanen Sakkwato na Alu ne da Buhari ne."
Wannan ya sha bambam da tunanin da ake yi na cewa yana kan hanyar barin jam'iyyar APC.
Duk wanda yasan siyasar Sakkwato, idan yaji mutum ya fita daga jam'iyyar Alu da Buhari yake ciki, yasan wata kaddarar ce ta fada mishi. Inji Wamakko.
DUBA WANNAN: Ina nan tare da Mai gidana a APC - Direban Lai Mohammed
Idan zamu tuna, jiya Laraba ne Gwamnan Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya sanar da fitarsa daga jam'iyyar APC, jam'iyyar da aka zabe shi karkashin inuwarta.
A jawabin da yayi wa magoya bayan shi, yace dalilin fitar sa daga jam'iyyar shine babu wani aikin cigaba da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai jihar sa.
Wamakko yace Tambuwal abin tausayi ne, ballantana da yaga yaro karami yana gaggawa a harkar rayuwa.
Tuni jama'ar Sakkwato suka dena jam'iyya, cancanta suke bi. Idan mutum yace ya bar Buhari da Alu, toh ya zama abin tausayi. Inji Wamakko.
Wamakko ya kara da cewa jam'iyyar APC ce zata kafa Gwamnatin Sakkwato kuma Buhari zai lashe jihar. Ra'ayin Sakkwato APC ne da Buhari, don haka Alu ba zai sabawa jama'ar shi ba.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng