El-Rufai ya tunbuke wani Sarkin gargajiya a jihar Kaduna

El-Rufai ya tunbuke wani Sarkin gargajiya a jihar Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da sauke wani Sarkin gargajiya na kauyen Fadan Kwoi a karamar hukumar Jaba dake jihar Kaduna, mai suna Malam Iliya Bako

El-Rufai ya tunbuke wani Sarkin gargajiya a jihar Kaduna

El-Rufai ya tunbuke wani Sarkin gargajiya a jihar Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da sauke wani Sarkin gargajiya na kauyen Fadan Kwoi a karamar hukumar Jaba dake jihar Kaduna, mai suna Malam Iliya Bako.

A wata takarda da kwamishinan kananan hukumomi da al'amuran sarauta, Farfesa Kabir Mato, ya bada, bai sanar da dalilin cire Sarkin ba.

DUBA WANNAN: Wata Sabuwa: Kotu ta sakawa El-Rufai doka akan rikicin sa da Sanata Hunkuyi

Takardar tace sarkin Jaba, Kpop Ham, Mista Danladi Maude, ya tura sunayen mutane uku da gwamnati zata zaba don ya maye gurbin.

Kamar yanda takardar tace, za a sanar da sunan sabon Sarkin bayan an kammala duk shirye shiryen da ya kamata.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel