Wata Sabuwa: Kotu ta sakawa El-Rufai doka akan rikicin sa da Sanata Hunkuyi

Wata Sabuwa: Kotu ta sakawa El-Rufai doka akan rikicin sa da Sanata Hunkuyi

Wata babbar Kotu a jihar Kaduna ta bada umarnin tsayar da hukumar tsara fili da gidaje ta jihar Kaduna wato (KASUPDA) akan shirin da take yi na yin gini akan filin Sanatan jihar Suleiman Hunkuyi

Wata Sabuwa: Kotu ta sakawa El-Rufai doka akan rikicin sa da Sanata Hunkuyi

Wata Sabuwa: Kotu ta sakawa El-Rufai doka akan rikicin sa da Sanata Hunkuyi

Wata babbar Kotu a jihar Kaduna ta bada umarnin tsayar da hukumar tsara fili da gidaje ta jihar Kaduna wato (KASUPDA) akan shirin da take yi na yin gini akan filin Sanatan jihar Suleiman Hunkuyi.

Kotu ta bada umarnin tsayar da duk wani shiri da hukumar take yi akan filin, wanda yake mai lamba 11B Sambo Road, Unguwan Rimi, Kaduna.

DUBA WANNAN: An kama barayin da suka kashe tsohuwar Kwamishinar 'Yan sandan jihar Katsina

Hukumar KADGIS ce ta kwace gidan, inda daga baya gwamnati ta bayar da umarnin a rushe shi, inda gwamnatin take zargin Sanatan da kin biyan kudin haraji na tsawon shekaru da yawa.

Mai Shari'a H.T.D. Gwadah, shine ya bada umarnin tsayar da aikin inda kuma ya daga sauraron karar har zuwa ranar 23 ga watan Oktobar wannan shekarar.

Majiyarmu Legit.ng ta samu rahoton cewar hukumar KADGIS ta mikawa hukumar KASUPDA filin da nufin a gina wurin wasan yara.

Daga baya Sanatan bai yi na'am da hukuncin da gwamnatin jihar ta dauka ba, inda shida Lauyan shi Farfesa Dankofa Yusuf suka nufi kotu da burin ta dakatar da duk wani yunkuri da gwamnatin jihar ta ke yi akan filin.

A ranar 20 ga watan Fabrairun wannnan shekarar ne gwamnatin jihar Kaduna karkashin mulkin Mal. Nasir Ahmad El-Rufai ta bada umarnin rushe gidan Sanata Suleiman Hunkuyin, inda wannan mataki ya kawo cece-kuce a tsakanin al'umma.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel