2019: Ku zama cikin shirin yaki - Secondus ga masu sauya sheka zuwa PDP

2019: Ku zama cikin shirin yaki - Secondus ga masu sauya sheka zuwa PDP

Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus, a daren ranar Larabar da ta gabata cikin birnin Abuja, ya zayyanawa wadanda suka sauya sheka ta ficewa daga jam'iyyar APC akan su kasance cikin shirin fafata gagarumin yaƙi.

Yake cewa, sai an kai ruwa rana tare da gudanar da baƙin gumurzu kafin a cimma nasarar ƙwato mulki daga jam'iyyar adawa ta APC, domin kuwa samun galaba a kanta ba abu ne da zai samu cikin sauƙi ba.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, Secondus ya bayyana hakan ne a babban birnin kasar nan tarayya yayin liyafar lale maraba da shugabannin jam'iyyar suka yiwa shiryawa 'yan majalisar tarayya da suka sauya sheƙa ta ficewa daga jam'iyyar APC zuwa PDP.

Kazalika rahotanni sun bayyana cewa, jam'iyyar za ta gudanar da taron shugabannin ta a yau Alhamis domin tabbatar da marabar su ga wadanda suka sauya sheƙa zuwa jam'iyyar ta su.

2019: Ku zama cikin shirin yaki - Secondus ga masu sauya sheka zuwa PDP
2019: Ku zama cikin shirin yaki - Secondus ga masu sauya sheka zuwa PDP

A yayin liyafar tande-tande da makwalashe, Secondus ya tabbatar da wadanda suka sauya sheƙa a matsayin jarumai da suka gaza hakurin bayyana fusatar su dangane da mulkin kama karya da ake gudanar wa cikin ƙasar nan.

KARANTA KUMA: Hukumar 'Yan sanda ta bukaci 'yan siyasa a Jihar Kano da su guje wa tayar da tarzoma da kalaman nuna ƙiyayya

Secondus ya ci gaba da cewa,babu waa mafi dacewa da ranar samun 'yancin kai face ranar da 'yan majalisar tarayya suka sauya sheƙa ta ficewa daga jam'iyyar APC. Ya bayyana damuwar sa dangane yadda a kullum gwamnatin tarayya ke iƙirarin sanin ababen dake faruwa a ƙasar nan.

Ya kuma kara da cewa, sauyin sheƙar da suka auku cikin jihohin Kwara, Sakkwato, Kogi da kuma jihar Kano alama ce ta tura da ta kai bango dangane da wahalhalun da 'yan najeriiya ke fuskanta karkashin mulki na jam'iyyar APC.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel