Da gangan Saraki ya dinga yiwa jam'iyyar APC zagon kasa - Lai Mohammed
A wata sanarwa da ofishin ministan yada labarai da al'adu na kasa ya fitar Alhaji Lai Muhammed ya ce ficewar Sanata Bukola Saraki daga jam'iyyar APC ba wata damuwa bace, kuma babu wata illa da hakan zai yiwa jam'iyyar ta APC a zaben 2019
A wata sanarwa da ofishin ministan yada labarai da al'adu na kasa ya fitar Alhaji Lai Muhammed ya ce ficewar Sanata Bukola Saraki daga jam'iyyar APC ba wata damuwa bace, kuma babu wata illa da hakan zai yiwa jam'iyyar ta APC a zaben 2019.
Ministan ya fitar da sanarwar ne a jiya Laraba, inda yake cewa jam'iyyar APC bata taba ga wani amfanin shugabancin Saraki ba, domin kuwa bata taba amfana da da shugabancin sa ba duk kuwa da kasancewar sa dan jam'iyyar APC.
DUBA WANNAN: 2019: Shugaba Buhari ya aikawa Mama Taraba wata wasika mai muhimmanci
"Inda ace Saraki ba dan jam'iyyar APC bane, da gwamnatin da jam'iyyar ke jagoranta baza ta sha wahalar data ke sha ba a yanzu, ganin irin yanda ya dinga sakawa ana samun jinkiri a wasu abubuwa na gwamnati, irin su kasafin kudi, manyan mukaman gwamnati da sauran su."
A ranar Talatar nan ne data gabata Sanata Bukola Saraki tare da gwamnansa na jihar Kwara suka bayyana sauya shekar su daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar PDP.
A bayanin da yayi lokacin ficewar tasa daga jam'iyyar, Saraki yace fitar tasa daga jam'iyyar ta zama dole, ganin yanda wasu manya daga cikin jam'iyyar APC din suka rufe duk wata hanya da zata tabbatar da zaman lafiya, hadin kai da kuma fahimtar juna a cikin jam'iyyar.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng