Allah ka shige mana gaba a wannan lokaci da muke – Ministan Buhari yayi addu’a a zaman majalisar zartarwa
Ministan bayanai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed a ranar Laraba ya nemi zabin Allah ga gwamnati mai ci “a wannan lokaci da Najeriya ke ciki.”
Mohammed ya fadi hakan ne a yayinda yake addu’an bude taro a zaman majalizar zartarwa da ake yi a duk mako a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari wadda ya dawo daga Lome, kasar Togo, inda aka nada shi a matsayin shugaban kungiyar ECOWAS ne ya jagoranci zaman.
An fara zaman ne wadda ya samu halartan mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo karfe 11am da yan mintoci kadan.
KU KARANTA KUMA: Ba zan sauya sheka daga APC ba – Mataimakin kakakin majalisa
Jam’iyyar APC ta sake samun Karin wadanda suka barta a ranar Talata, inda shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, Gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed da jakadan Najeriya a kasar Afrika ta Kudu, Alhaji Ahmed Ibeto suka koma PDP.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng