Yaki da Boko Haram: Rundunar Sojojin Najeriya ta hada kai da mafarauta da yan tauri

Yaki da Boko Haram: Rundunar Sojojin Najeriya ta hada kai da mafarauta da yan tauri

Rundunar dakarun Sojin kasa ta bayyana bukatar hadin kai da aiki tare da kungiyar mafarauta da yan kato da gora don kawo karshen ayyukan ta’addanci a jihar Borno, da sauran jihohin dake yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

Legit.ng ta ruwaito babban kwamandan runduta ta bakwai dake Borno, Birgediya Janar Abdulmalik Biu ne ya bayyana haka a yayin ganawa da yayan kungiyar da suka kai masa ziyara a ofishinsa dake garin Maiduguri, a karkashin jagorancin shugabansu, Alhaji Maigana Maidarma.

KU KARANTA: Kwankwaso da Ganduje sun yi haduwar farko tun bayan ficewar Kwankwaso daga APC

Yaki da Boko Haram: Rundunar Sojojin Najeriya ta hada kai da mafarauta da yan tauri
Taron

Biu ya jinjina ma mafarautan bisa kwarewarsu a fagen farauta, sa’annan yayi mamakin yadda suke da ilimin dazukan jihar, inda yace taron zai basu damar tattauna batutuwan lalubo hanyoyin kawo karshen ta’addan a yankin.

Daga karshe Janar Biu ya bayyana ma mafarautan cewa zasu samu goyon baya daga kwamandojin yaki dake bakin daga, sa’annan ya bukaci da su taimaka ma rundunar da ingantattun bayanai da zasu taimaka wajen yaki da yan Boko Haram.

A nasa jaawabin, shugaban mafarautan, Alhaji Maigana ya tabbatar da goyon bayansu ga rundunar Sojin, inda ya yi alkawarin zasu taimaka ma Sojojin da bayanai game da dajin Sambisa, sai dai ya koka kan rashin ababen hawa da makaman da zasu yi amfani dasu a duk lokacin da suka yi kicibus da Boko Haram.

Yaki da Boko Haram: Rundunar Sojojin Najeriya ta hada kai da mafarauta da yan tauri
Taron

Bugu da kari, shugaba Maigana ya yaba da shugabancin babban hafsan rundunar Sojin kasa, Laftanar janar Tukur Yusuf Buratai, inda yace ba’a taba samun jajirtaccen shugaban Soji kamarsa ba tun da aka fara yaki da Boko Haram.

Daga karshe Janar Biu ya mika wasu kayayyaki a matsayin tallafa ga kungiyar don taimaka musu a aikin da suke gudanarwa, da suka hada da ruwan gora, jarkokin man gyada da sauran kayan abinci.

Yaki da Boko Haram: Rundunar Sojojin Najeriya ta hada kai da mafarauta da yan tauri
Taron

Daga cikin wadanda suka halarci zaman akwai manyan hafsoshin Soji dake jihar Borno, sakatern kuniyar mafarauta, Bunu Bukar, shugaban mata ta kungiyar mafarauta, Hajiya Maira Mai-Durma, da kuma mafarauta da dama.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng