Kwankwaso da Ganduje sun yi haduwar farko tun bayan ficewar Kwankwaso daga APC

Kwankwaso da Ganduje sun yi haduwar farko tun bayan ficewar Kwankwaso daga APC

A wani yanayi na bambarakwai, an yi wata haduwar bazata tsakanin Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, da tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a jihar Kaduna, amma fa babau wanda yace ma wani uffan.

Legit.ng ta ruwaito tsofaffin aminan sun hadu ne a yayin jana’izar uwargidar Janar Aliyu Muhammad Gusau, ranar Talata 31 ga watan Yuli, wanda aka binneta a wata makabarta dake garin Kaduna, sai dai duk da cewa sun hadu gab da gab a makabartar, amma basu yi magana da juna ba.

KU KARANTA: Likafa ta cigaba: Shugaba Buhari ya zama shugaban kungiyar kasashen yammacin Afirka

Kwankwaso da Ganduje sun yi haduwar farko tun bayan ficewar Kwankwaso daga APC
Kwankwaso da Ganduje

Wannan haduwa itace haduwar farko da jigogin siyasar jihar Kano suka yi tun bayan ficewar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso dsaga jam’iyyar APC, inda ya hada kai da tsohon gwamnan jihar, Ibrahim Shekarau a jam’iyyar PDP don kawar da Ganduje a zabe mai zuwa.

Marigayiya Hajiya Binta Gusau ta rasu ne a ranar Juma’a 27 ga watan Yuli a wani Asibtin kasar Jamus bayan ta yi fama da doguwar jinya, hakan yasa aka sa aka samu jinkirin dawo da gawarta Najeriya, har sai ranar Talata.

Kwankwaso da Ganduje sun yi haduwar farko tun bayan ficewar Kwankwaso daga APC
Ganduje da Ali Gusau

Daga cikin wadanda suka halarci jana’izar akwai gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, gwamnan Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki, mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Ibrahim Wakkala, Gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello da dai sauransu.

Kwankwaso da Ganduje sun yi haduwar farko tun bayan ficewar Kwankwaso daga APC
Jana'izar

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng