Wanke Bafarawa: EFCC ta hau kujerar na ki, ta ce ba zata kyale ba
A yau, Talata, ne Jastis Bello Abbas na kotun Sokoto ya wanke tsohon gwamnan jihar Sokoto Alhaji Attahiru Bafarawa daga tuhumar da ake masa na rashawar naira biliyan 115 tare da wasu mutane uku.
Yayinda yake yanke hukuncin, Jastis Abbas ya bayyana cewa dukkanin hujjojin da aka gabatar gaban kotu basu nuna Attahiru Bafarawa a matsayin mai laifi ba sannan kuma basu wanke shakku ba.
A nasa bangaren lauyan mai kara, Barista Jacob Ochidi ya yabama kotu da ta bi tsare-tsaren da suka dace a a hukuncinta.
Saidai a wani sako da hukumar yaki da cin hanci da yiwa tattalin arziki ta'annati (EFCC) ta fitar ta shafinta na Tuwita, ta bayyana cewar tayi matukar mamakin hukuncin da kotun ta yanke tare da bayyana cewar tuni ta garzaya kotun daukaka kara domin kalubalantar hukuncin. EFCC ta ce kada ma tsohon gwamnan ya dauka ya ci bulus.
A ranar 8 ga watan Mayu ne mai shari’a Abbas ya tsayar da yau, 4 ga watan Yuli, a matsayin ranar da zai yanke hukunci a shari’ar da aka shafe shekaru 9 ana fafatawa.
DUBA WANNAN: Ofireshon Lafiya Dole: Manjo Janar Abba Dikko ya maye gurbin Rogers Nicholas
Saidai yayin zaman kotun na ranar 4 ga watan, sai alakalin kotun ya yi bulaguro domin gudanar da wani aiki, amma ya saka ranar 31 ga watan Yuli a matsayin ranar da za a dawo domin sauraron hukuncin da kotun zata yanke.
Bafarawa na fuskantar tuhuma da 33 da suka jibanci cin hanci, sayar da hannayen jarin gwamnati ba bisa ka’ida ba, almundahana, karbar kayan sata, da kuma biyan kudi ba bisa ka’ida bag a wasu kamfanonin bogi yayin da yake gwamna tsakanin shekarar 2003 zuwa 2007.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng