Labarin dan Najeriyan da ya cirewa wata mai ciki gyambo sannan ya mayar da dan cikinta ya dinke

Labarin dan Najeriyan da ya cirewa wata mai ciki gyambo sannan ya mayar da dan cikinta ya dinke

- An sake sake samun wani kwararren likita dan Najeriya da yayi wani abin mamaki

- Ya fede wata mata yayin da take dauke da juna biyu sannan ya mayar da jaririn cikin uwarsa

- A karshe kuma ta haifi abinta lafiya kalau

Sau da dama akan bayar da labarin ‘yan Najeriya da suka yi fice ko wani abin bajinta, musamman a kashashen ketare.

A nan ma wani kwararren likita ne dan asalin Najeriya ya ceto rayuwar wata mata mai juna biyu ta hanyar yi mata fida, mai cikin dai ya rage mata saura sati 36 ne ta haihu amma saboda ciwon gyambon ciki da yake damunta a yayinda cikinta yake matsayin sati 23 ya zama tilas a cire shi.

Bajinta: Labarin dan Najeriyan da ya cirewa wata mai ciki gyambo sannan ya mayar da dan cikinta ya dinke
Bajinta: Labarin dan Najeriyan da ya cirewa wata mai ciki gyambo sannan ya mayar da dan cikinta ya dinke

Hakan ta sanya wannan kwararren likitan dan asalin Najeriya mai suna Dr. Oluyinka Olutoye yi mata tiyartar inda ya cire dan nata gefe guda sannan ya cire mata gyambon cikin da yake damunta kana ya mayar da dan cikin nata ya dinke.

KU KARANTA: Karen hauka ya ciji wani matashi, ya kashe Ubansa da kaninsa

Kwanci tashi matar ta murmure sarai har lokacin haihuwarta yayi ta hafi jaririyarta sumul cikin koshin lafiya da kanta ba tare da an yi mata fida ba.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng