Wani mummunan hadari yayi sanadiyyar mutuwar mutum 6, yayinda 69 suka ji munanan raunuka

Wani mummunan hadari yayi sanadiyyar mutuwar mutum 6, yayinda 69 suka ji munanan raunuka

Kimanin mutane 6 ne suka rasa rayukan su, inda sama da mutane 69 suka ji munanan raunuka sakamakon wani mummunan hadari daya auku a karamar hukumar Kwali, dake babban birnin tarayya Abuja

Wani mummunan hadari yayi sanadiyyar mutuwar mutum 6, yayinda 69 suka ji munanan raunuka
Wani mummunan hadari yayi sanadiyyar mutuwar mutum 6, yayinda 69 suka ji munanan raunuka

Kimanin mutane 6 ne suka rasa rayukan su, inda sama da mutane 69 suka ji munanan raunuka sakamakon wani mummunan hadari daya auku a karamar hukumar Kwali, dake babban birnin tarayya Abuja.

Wani wanda hadarin ya auku a gabashin ya bayyana cewar lamarin ya faru ranar Lahadi ne da dare a kan kwanar kasuwar Kwali dake kan babbar hanyar Abuja zuwa Lokoja, inda wata mota mai kirar Luxurious ta fadi wacce aka fi sani da suna Marcopolo.

DUBA WANNAN: EFCC ta kama wani gwamna a arewa ya cinye sama da naira biliyan 20

Mutumin yace motar wacce take da rijistirashin lamba AWK 426 YE ta fada wani rami a dai-dai lokacin da direban motar yaso ya wuce wata babbar mota.

Ya ce direban motar yayi kokarin wuce wani mai babbar mota, inda motar ta kwace a hannun sa ta fada cikin wani babban rami, sanadiyyar da mutane 6 suka mutu kenan.

Mutumin ya kara da cewa jami’an hukumar kiyaye hadura na kasa sune suka fito da gawarwakin sannan suka kai wadanda suka ji ciwo asibiti.

Shugaban hukumar kiyaye hadura na Yangoji, ACC Joseph Samgbaza, ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya alakanta hakan da gudun ganganci.

Ya ce an wuce da gawarwakin babban asibiti na garin Kwali, yayinda su kuma marasa lafiyan aka kai su asibitocin, Rhema Clinic, Kwali da kuma St. Mary Catholic Hospital dake Gwagwalada.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng