Buhari ya aika a kawo masa Limamin da ya boye Kiristoci a lokacin fadan Filato
Kwanakin baya ne rikici ya barke a Garin Jos tsakanin Fulani da ‘Yan Kabilar Birom wanda hakan ya ci daruruwan mutane a a Jihar ta Filato. An samu wani Bawan Allah Musulmi da ya ceci al’umma da dama a lokacin wancan rikici.
Wani Dattijon Limami mai shekaru kusan 83 zai gana da Shugaba Muhammadu Buhari a fadar Shugaban kasa saboda irin abin da yayi. Wannan Limami dai ya ba Kiristoci sama da 300 mafaka domin gudun Jama’a su kashe su.
A karshen watan jiya ne wannan Limami mai suna Abdullahi Abubakar ya boye Matan Kiristoci a cikin gidan sa domin hana Fulani su far masu. Limamin ya kuma boye Maza ne a cikin Masallacin da yake limanci inji Daily Nigerian.
KU KARANTA: Dakarun Sojoji sun cafke wasu 'yan fashi dake basaja cikin kaki
Wannan abu dai ya faru ne a wani Kauye da ake kira Nghar da ke Yankin Gashish a cikin Karamar Hukumar Barkin Ladi da ke cikin Filato. Imam Abdullahi zai gana da Shugaba Buhari domin kasa ta yabawa kokarin nan na sa.
Shugaban kasa Buhari ya ba Gwamnan Filato Simon Lalong umarni a kawo masa wannan Limami domin ya gaisa da Shugaban kasa kuma a karrama sa da lambar yabo na kasa. Wannan Shehi dai yayi kokari na kare rayukan al’umma.
Fulani sun nemi kashe Kiristocin Yankin amma wannan Limami ya hana. Bayan aukuwar abin ne idan ba ku manta ba Shugaban kasa Buhari da kuma Yemi Osinbajo su taka da kan su zuwa Jihar ta Filato.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng