Bacin rana: Wasu 'yan fashi da dake basaja cikin kaki sun yi arangama da dakarun soji, hotuna
Rundunar soji dake aikin mayar da martani cikin gaggawa (Quick Response Force) tayi nasarar cafke wasu 'yan fashi da makami a Felele dake kan hanyar Lokoja zuwa Okene.
'Yan fashin sun yi basaja cikin kakin sojoji domin yaudarar matafiya su dauka jami'an tsaro ne.
Hukumar sojin kasa, ta bakin Texas Chukwu, darektan yada labarai, ta ce ta yi nasarar kama uku daga cikin 'yan fashin, Savior Denis - mai shekaru 39, Isaac Donald - mai shekaru 35, da kuma Joseph Isah - mai shekaru 35, yayin da daya daga cikinsu, Mista Arten ya rasa ransa yayin musayar wuta da dakarun soji.
Kazalika an kama wasu mata biyu, Janet Isah da Oyinoye Ochefije dake taimakon 'yan fashin.
Kayayyakin da aka samu a wurin fashin sun hada da; Bindiga samfurin AK-47 guda daya, jigidar harsashin AK-47 mai zagaye 28, kakin sojoji 8, adda guda daya, wayoyin hannu 22, kudi N16,000 da sauran su.
DUBA WANNAN: An rushe shugabannin APC na jihar Kwara, an nada sabbi
Yanzu haka 'yan fashin na hannun jami'an soji inda suke amsa tambayoyi kafin daga bisani a mika su ga hukumar da ya dace domin daukan mataki na gaba a kansu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng