Wasu manyan Sanatocin Arewa sun koka game da rikicin Zamfara

Wasu manyan Sanatocin Arewa sun koka game da rikicin Zamfara

- Kwankwaso ya sa baki bayan an kashe Bayin Allah a Jihar Zamfara

- Sanatan na Jihar Kano yace kashe rayukan jama’a a Kasar yayi yawa

A jiya ne mu ka samu labari cewa Sanatan Kano Rabiu Musa Kwankwaso yayi magana game da yadda sha’anin tsaro ya tabarbare musamman a Jihar Zamfara da ke cikin Arewacin Najeriya.

Wasu manyan Sanatocin Arewa sun koka game da rikicin Zamfara

Kwankwaso ya sa baki bayan an kashe mutane a Zamfara

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso wanda kwanan nan ya fice daga Jam’iyyar APC ya dawo PDP yayi amfani da shafin sa na sada zumunta da watsa bayanai watau Tuwita ya koka game da munanan kashe-kashen da ake yi a Jihar Zamfara.

Tsohon Gwamnan na Kano ya koka cewa yanzu har kisan rai ya zama ba komai ba a Yankin Zamfara saboda yadda harkar tsaro ya tabarbare a cikin Najeriya. Sanatan yace abin ta kai har jama’a sun saba da jin labarin kashe-kashe a kasar.

KU KARANTA: Wasu Gwamnonin APC sun fara hangen kujerar Sanata

Kwankwaso yayi wannan bayani ne bayan an kashe Bayin Allah da dama kwanan nan a Jihar Zamfara inda ya nemi Gwamnati ta yi abin da ya dace na kare rayukan al’umma. Yanzu dai Shugaban kasa ya aika Jami’an Sojoji 1000 Yankin.

Kafin nan ma dai Sanatan Kaduna ta tsakiya Shehu Sani yayi tir da wannan abu da yake faruwa a Arewacin kasar. An koka da yadda ake kashe al’umma dare-da-rana a cikin Arewacin Najeriya inda Mutane su ka kai kuka wajen Shugaban kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel