Wasu Sanatocin Najeriya sun ce Shugaba Buhari bai da tamka a zaben 2019
Mun samu jin labarin cewa wasu manyan ‘Yan Majalisa a Najeriya su na da ra’ayin cewa babu ‘Dan siyasar da zai iya karawa da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kwana lafiya a zaben 2019. Daga cikin ‘Yan Majalisun akwai:
1. Bukar Abba Ibrahim
Sanata Bukar Abba Ibrahim na Jihar Yobe ya bayyana cewa Shugaba Buhari zai iya ja da kowa kuma ya kwana lafiya. Sanatan na Yobe ta Gabas yace duk da sauya-sauyan shekar da wasu ke yi Buhari zai yi nasara.
KU KARANTA: Shekarau da Kwankwaso sun yi wani zama na musamman a Abuja
2. Ali Ndume
Shi ma Sanata Ali Ndume na Borno ta Kudu yana ganin cewa babu wanda zai doke Shugaba Buhari a 2019 saboda irin kokarin da yayi wa Talakawa wajen irin su aikin N-Power da harkar noma a kasar.
3. Chile Okafor
Honarabul Chile Okafor wanda ke wakiltar Yankin Ihitte/Obowo/Uboma ya bayyana cewa Shugaba Buhari mutum ne mai gaskiya kuma babu wanda zai iya tinkarar sa a filin zabe ko ‘Dan wa PDP ta tsaida.
Kun ji labari cewa wani Sanatan APC ya bayyana abin da ya shiryawa Saraki a fadar Shugaban kasa saboda cin amanar Buhari da yayi. Sanatan yace wadanda su ka koma Jam’iyyar PDP sun fado ta ka a siyasa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng