2019: Wadanda su ka koma Jam’iyyar PDP sun fado ta kai inji Sanatan APC

2019: Wadanda su ka koma Jam’iyyar PDP sun fado ta kai inji Sanatan APC

Mun ji labarin cewa wani babban Sanatan a Jam’iyyar APC mai mulki ya bayyana abin da ya shiryawa Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki idan da ya halarci zaman su da Shugaban kasa Muhammadu Buhari na kwanakin baya.

2019: Wadanda su ka koma Jam’iyyar PDP sun fado ta kai inji Sanatan APC

Sanata Abdullahi Adamu yace Saraki ya ci amanar Buhari

Abdullahi Adamu da ke wakiltar Yammacin Nasarawa a karkashin Jam’iyyar APC yace da ace sun yi ido-biyu da Bukola Saraki a fadar Shugaban kasa da ya kore sa daga wajen taron inda ‘Yan Majalisar APC su ka hadu da Buhari.

Sanatan ya bayyana cewa duk ‘Yan Majalisar da su ka sauya-sheka zuwa Jam’iyyar adawa ta PDP ba su yi lissafi da kyau ba. Sanatan na Nasarawa yace wasu ‘Yan uwan na sa da su ka bar APC sun tafka babban kuskure a lissafin siyasar su.

KU KARANTA: Buhari zauna Kwankwaso domin hana sa barin APC

‘Dan Majalisar ya bayyana cewa wasu Sanatocin na APC dama can ‘Yan PDP ne inda yace da gangan aka kirkiro R-APC. Sanata Adamu ya fadawa Daily Trust cewa a wata hira cewa idan har Saraki ya koma PDP, dokar kasa tace dole ya bar kujerar sa.

Sanata Abdullahi Adamu yace Bukola Saraki ya ci amanar Shugaban kasa Buhari kuma da ya shigo taron su na kwanaki da ya ci masa mutunci. Doyin Okupe yana da ra’ayin cewa Saraki ba zai rasa mukamin sa ba ko da ya bar APC.

Dama kun san cewa Sanatocin APC kusan 10 su ka yi watsi da gayyatar Shugaba Buhari na wani taro kwanaki. An nemi wasu manyan ‘Yan Majalisar APC irin su Shugaban Majalisa Bukola Saraki wajen wani zama a Aso Villa an rasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel