Rayuka 42 sun salwanta a wani sabon hari cikin jihar Zamfara

Rayuka 42 sun salwanta a wani sabon hari cikin jihar Zamfara

A ranar Juma'ar da ta gabata ne 'yan ta'adda rike da makamai sukaa sheke mutane 42 yayin da suka kai hari wasu kauyuka 18 karkashin mazabun Mashema, Kwashabawa da Birane dake karkashin karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.

Rahotanni kamar yadda shafin jaridar Daily Nigerian ta ruwaito sun bayyana cewa, adadin rayukan da suka salwanta na iya zarce 100 a yayin da mutane da dama suka bace bayan da 'yan ta'addan suka dira a kauyukan.

Wani mashaidin wannan mugun gani da mugun ji, Lawwali Mashema ya bayyana cewa, dubunnan al'umma daga garin na Zurmi sun yi gudun neman tsira har na tsawon kilomita 50 daga muhallan su domin tseratar da rayukan su.

Da yawan wadanda suka tseratar da rayukan sun yi gudun hijira tare da neman matsugunnin a makociyar jiha ta Katsina yayin da wasun su suka ketare zuwa jamhuriyyar Nijar.

A yayin ziyarar sa, Mataimakin gwamnan jihar Mallam Ibrahim Muhammad Wakkala ya bayyana cewa, wannan hari da ya salwantar da rayukan mata, kananan yara da kuma dattijai ya yi matukar muni wanda ba ya da ma'auni face na zalunci.

KARANTA KUMA: Masari ya nemi ma'aikatan sa kan zage dantse wajen gudanar ayyukan su

Wakkala wanda ya wakilci gwamnan jihar, ya sha alwashin daukar matakai da zasu kawo karshen wannan annoba dake ci gaba da ta'azzara a jihar.

Shugaban kungiyar bayar da agaji na jihar kuma kakakin majalisar jihar, Sanusi Rikiji, ya yi kira kan tsananta ingancin tsaro a yankin da wannan ibtila'i ya afku.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng