Sarki Ali Nuhu ya bawa gwamna Ganduje kyautar lambar yabo, duba hoto

Sarki Ali Nuhu ya bawa gwamna Ganduje kyautar lambar yabo, duba hoto

Fitaccen jarumin wasannin shirin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Ali Nuhu, ya gabatar da kyautar lambar yabo ga gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahu Umar Ganduje.

Ali Nuhu ya mika kyautar ne ga gwamna Ganduje da yammacin yau, Asabar, a fadar gwamnatin jihar Kano yayin gabatar da wani shirin wasan Hausa, MUTUM DA ADDININ SA, da aka shirya domin karfafa gwuiwa da ilimantar da jama’a a kan hakuri da juriyar zama da wadanda ba addininsu daya ba.

Sarki Ali Nuhu ya bawa gwamna Ganduje kyautar lambar yabo, duba hoto

Sarki Ali Nuhu ya bawa gwamna Ganduje kyautar lambar yabo

A wani labarin na Legit.ng kun ji cewar shugaba Buhari ya bukaci magoya bayansa da su sassauta da yi masa yakin neman zaben shekarar 2019 domin yin hakan sabawa dokar hukmar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ne.

DUBA WANNAN: Daya daga cikin tsofin gwamnonin PDP ya fice daga jam'iyyar

A jawabin da mai ba shi shawara a bangaren yada labarai, Femi Adesina, ya fitar a yau, Asabar, Buhari ya bukaci magoya bayansa da su yi hakuri da yi masa kamfen har sai lokacin da doka ta yarda a fara yakin neman zabe tare da shawartarsu das u cigaba da tallata aiyuka da nasarorin da gwamnatinsa ta samu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel