Asarar da Ambaliyar ruwa ta janyo a jihar Kebbi ta girgiza ni - Buhari
A yau Asabar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajantawa al'ummar jihar Kebbi dangane da aukuwar ambaliyar ruwa da ta yi sanadiyar lalata gonaki gami da amfanin gona da kuma gidajen al'umma.
Buhari ya bayyana sakon ta'aziyyar sa cikin wata sanarwa da babban hadiman sa na musamman, Mallam Garba Shehu ya bayyana wa manema labarai.
Shugaba Buhari yake cewa, ya yi matukar girgiza a sakamakon girman asarar da ambaliyar ruwa ta yi sanadi ga manoma a jihar Kebbi.
Rahotanni sun bayyana cewa, gwamnatin shugaba Buhari ta shiga cikin damuwa dangane da aukuwar wannan annoba sakamakon muhimmiyar rawa da jihar Kebbi take takawa musamman yadda ta yiwa sauran jihohin Najeriya dukan kece raini tare da fintinkau wajen samar da shinkafa.
Baya ga samar da ayyukan yi da abin dogaro ga manoma, Buhari ya lura da cewar harkokin noma na da tasirin gaske wajen habakar tattalin arziki cikin kasar nan.
KARANTA KUMA: 2019: Na fi kowa cancantar Tikitin takara na jam'iyyar PDP - Lamido
Buhari ya nemi manoman da annobar ta afkawa akan kada su gaza ko su karaya, inda ya bayar da tabbaci a gare su da cewar gwamnatin sa ba za ta manta da wannan hali na tagayyara da suka shiga a halin yanzu.
Ya kuma yabawa gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamna Abubakar Atiku Bagudu, dangane da matakai masu tasirin gaske da ya dauka cikin gaggawa domin kawo sauki da rarrashi na sanyaya zukatan manoman da aukuwar annobar ta shafa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng