Da dumi-dumi: Shuagaba Buhari zai tashi zuwa birnin Lome a yau, duba jerin ‘yan rakiyar sa

Da dumi-dumi: Shuagaba Buhari zai tashi zuwa birnin Lome a yau, duba jerin ‘yan rakiyar sa

A yau, Lahadi, ne shugaba Buhari zai tashi birnin Lome na kasar Togo inda zai halarci wani taron kungiyar kasashen Afrika (ECOWAS).

Shugaba ya zabi gwamnan jihar Kuros Riba, Farfesa Ben Ayade, da takwaransa na jihar Neja, Sani Bello, a matsayin gwamnoni da zasu raka shi.

Ragowar jami’an gwamnati da zasu kasance cikin tawagar shugaba Buhari sun hada da ministan harkokin kasashen waje, Geofrey Onyeama, takwaransa na harkokin cikin gida, Abdulrahman Dambazau, ministan tsaro, Mansur Dan-Ali, da kuma na masana’antu da kasuwanci.

Da dumi-dumi: Shuagaba Buhari zai tashi zuwa birnin Lome a yau, duba jerin ‘yan rakiyar sa
Da dumi-dumi: Shuagaba Buhari zai tashi zuwa birnin Lome a yau

Mai bawa shugaban kasa a kan harkokin tsaro, Babagana Munguno, shugaban askarawan soji na kasa, Abayomi Olanisakin, shugaban hukumar tsaro ta NIA, Ahmed Abubakar da gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emefiele, na cikin tawagar shugaba Buhari zuwa taron na ECOWAS.

Ana saka rai a karshen taron za a zabi shugaban kungiyar ECOWAS da zi karba daga hannun wanda ke kai yanzu, kuma ya dauki nauyin taron.

DUBA WANNAN: Buhari ya bukaci a dakatar da yakin neman zabensa, duba dalili

Taron na wannan karo zai mayar da hankali ne kan tattauna batutuwan da suka shafi tsaro a kasashen Guine Bisau, Mali da kuma Togo.

Yayin ziyarar shugabannin Najeriya a kasar ta Togo, shugaba Buihari zai tattauna da ragowar shugabannin kasashen Afrika a kan yadda za a kirkiri takardar kudi ta bai daya ga kasashen dake cikin kungiyar ECOWAS. Ana saka ran kamala maganar kirkirar sabon kudin a shekarar 2020

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng