2019: Na fi kowa cancantar Tikitin takara na jam'iyyar PDP - Lamido
A ranar Juma'ar da ta gabata ne tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya kaddamar da kansa a matsayin dan takara daya tilo da ya cancanci tikitin takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP da zai fafata a zaben 2019.
Lamido ya jaddada cewa, cikin dukkanin masu hankoron kujerar shugaban kasa shi kadai ne mai matabbaciyar akida ta jam'iyyar PDP da babu wata tantama a cikin ta.
Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne yayin ganawa da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP a jihar Bayelsa, inda ya ke bugun gaba gami da alfaharin kasancewa zakaran gwajin dafin da jam'iyyar za ta tsayar da shi a matsayin dan takarar ta a zaben 2019.
Da sanadin shafin jaridar The Nation mun samu rahoton cewa, Lamido ya ziyarci jihar Bayelsa ne domin neman goyon bayan jam'iyyar PDP reshen jihar tare da zayyana kudirin sa na neman kujerar shugaban kasa.
Tsohon gwamnan ya kuma bayyana cewa, shi kadai ne dan takarar da jam'iyyar PDP za ta tsayar da yake da cancantar kalubalantar shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019.
KARANTA KUMA: Wata Mahaifiya ta manta jaririn dan watanni 3 cikin Mota, sai gawar sa ta tsinta
Legit.ng ta fahimci cewa, Alhaji Lamido ya ziyarci jihar Bayelsa ne domin kaddamar da wasu ayyuka, inda ya kuma muzantawa sauran masu hankoron kujerar shugaban kasa da cewar shi kadai ya ke da matabbaciyar akida ta jam'iyyar da ya cancanci tikitin takara.
A nasa bangaren, gwamnan jihar Seriake Dickson, ya yabawa Lamido dangane da wannan matabbaciyar akida da ya rika tun tala-tala ta jam'iyyar PDP, tare da jajircewar sa wajen goyon bayan ci gaban kasar nan.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng