Korarren direba ya dawo gida don yiwa maigidansa fashi, yace ramuwa ya zo

Korarren direba ya dawo gida don yiwa maigidansa fashi, yace ramuwa ya zo

Jami'an hukumar 'yan sandan kiyaye fashi da makami (FSARS), suny nasarar cafke tsohon direban wani Attajiri a Legas mai suna Utchay Odims a yayin da ya taho gidan tsohon mai gidansa domin yi masa fashi.

Lamarin ya afku ne a gida mai lamba 382 Demola Ajasa Street, Omoolo Estate a jihar Legas.

Leadership ta ruwaito cewa an attajirin, Odims ya dauke wanda aka kama wato Solomon James, aiki ne a watan Mayun wannan shekarar amma ya sallame shi daga aiki bayan kimanin wattani biyu a kan wata dalili da ba'a bayyana ba.

Korarren direba ya dawo gida domin fashi kan ogansa, yace ramuwa ya zo

Korarren direba ya dawo gida domin fashi kan ogansa, yace ramuwa ya zo

An gano cewa korar da aka yiwa Solomon bai masa dadi ba hakan yasa ya yi shiri ya koma gidan tsohon mai gidan nasa don yi masa fashi, abinda ya kira 'ramuwar gaya' a kan irin hakkinsa da tsohon mai gidan ya danne.

DUBA WANNAN: Kasashe 10 da suka fi talauci a nahiyar Afirka

Rahotanni sun bayana cewa Solomon ya afka gidan tsohon mai gidansa ne dauke da makami kuma da shigarsa sai ya tarar da mai aikin gidan kuma ya daure ta, daga nan ya kara gaba ya tarar da mai gidan kuma ya nemi ya fada masa inda matarsa take sai yace masa tayi tafiya.

Sai dai kafin Solomon ya kammala fashin ya bar gidan, anyi wa 'yan sanda waya kuma suka garzayo gidan inda suka cafke shi yayin da yake kokarin tsallake katanga.

Solomon ya amsa cewa ya shiga gidan tsohon mai gidansa amma wai ya tafi don yin ramuwar gayya ne. A cewarsa, dalilin da ya tambaya inda matar gidan take wai yana son ya fada mata cewa mai gidanta yana kwashe-kwashen mata a gari duk da cewa yana ikirin cewa shi fasto ne.

Solomon, ya kuma ce tsohon mai gidan nasa bai biya shi albashinsa ba na tsawon wattani biyu da ya yi masa aiki a matsayin direba sai dai ya rika mika masa 'yan canji yana masa alkawarin cewa zai biya shi.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Imohimi Edgal, ya tabbatar da afkuwar lamarin sai dai yace wannan fashi da makami ne ba wata ramuwar gayya ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel