Kotu ta tsige wani basarake dan gatan gwamnan jihar Adamawa
A yau Juma'a ne wata babban kotu dake zamanta a Yola karkashin jagorancin Justice Hafsat Abdulrahman da soke nadin da gwamnatin jihar ta yiwa Yarima Wakili a matsayin hakimin Jalingo-Maiha.
Kotun ta umurci Gwamna Muhammadu Bindow ya amince da Mahmud Abubakar wanda dama tun farko majalisar sarautar Mubi ta amince dashi a matsayin hakimi.
Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito cewa Mahmud Abubakar ya maka gwamnan jihar da Yarima Wakili da Alkalin Alkalan jihar bisa nadin da suka yiwa Wakili a matsayin hakimin Jalingo-Maiha a karamar hukumar Maiha.
DUBA WANNAN: Kasawar Buhari fa kasawar Arewa ce baki daya - Dattijan Arewa
A yayin da take yanke hukunci, Justice Abdulrahman tace wanda ya shigar da karar ya gamsar da kotu cewa shine ainihin wanda aka zaba a matsayin Hakimin Maiha a zaben da masu unguwani su kayi.
Hakan yasa kotun ta umurci gwamnatin jihar Adamawa ta rantsar da Abubakar a matsayin Mai Unguwan Jalingo-Maiha dake karamar hukumar Maiha tare da cewa nadin da a kayi wa Wakil kuskure ne kuma ta soke nadin.
Kotun har ila yau ta gargadi Wakili ya dena ambatar kansa a matsayin Mai Unguwar Jalingo-Maiha dake karamar hukumar Maiha na jihar Adamawa.
A baya, Legit.ng kawo muku rahoto inda shugaba jam'iyyar APC, Adams Oshiomhole ya gargadi 'yan majalisar APC cewa jam'iyyar ba zata bawa kowa tikiti ba tare da an gudanar da zaben fidda gwani ba.
Oshiomhole ya yi wannan jawabin ne yayin taron sa da 'yan majalisar a sakatariyar APC dake Abuja yayin da suka kai masa ziyara bayan ficewar wasu mambobin jam'iyyar zuwa jam'iyyar adawa ta PDP.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng