Dalilin da ya hana ni ficewa daga jam'iyyar APC - Shehu Sani
A ranar Alhamis din da ta gabata Sanatan nan mai wakilcin jihar Kaduna ta Tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Shehu Sani, ya bayyana cewa har ila yau yana nan a jam'iyya mai rike a gwamnatin kasar nan ta APC.
Sanatan ya bayyana hakan ne yayin amsa tamboyin manema labarai a shelkwatar jam'iyyar bayan ganawa da shugaban jam'iyyar na kasa gaba daya, Adams Oshiomhole.
Kamar yadda shafin jaridar Premium Times ya bayyana, Sanatan na ci gaba da goyon bayan tare da sa rai gami da kyautata zaton sa kan shugaban jam'iyyar dangane da samun nasarar fafutikar da yake ta sulhunta jam'iyyar.
Shehu ya ci gaba da cewa, yana da cikakken yakini da kuma aminci kan shugabancin jam'iyyar wajen sulhunta matsalolin da suka jam'iyyar su rikon kazar kuku a halin yanzu.
KARANTA KUMA: Kada ku zargi Shugabanni kadai da laifin yanayin da Najeriya take ciki a halin yanzu - Buhari
Legit.ng ta ruwaito cewa, a ranar Talatar da ta gabata ne wasu Sanatoci 14 suka fice daga jam'iyyar ta APC tare da sauya sheka zuwa wasu jam'iyyun adawa. Hakan ya sanya shugaba Buhari da ragowar sanatocin suka shiga cikin ganawa ta gaggawa a kashe garin rana ta Laraba.
A yayin tuntubar sa dangane da matsayar sa cikin jam'iyyar, Sanata Shehu ya bayyana har yanzu yana nan a cikin ta wanda da ba don hakan ba babu abinda zai kawo shi babban ofishin ta na kasa a halin yanzu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng