Wata Kotu ta tasa keyar yan fashi da makami guda 3 dake fakewa da sana’ar Achaba

Wata Kotu ta tasa keyar yan fashi da makami guda 3 dake fakewa da sana’ar Achaba

Wata Kotun majistri dake Ikeja na jihar Legas ta bada umarnin garkame mata wasu yan Achaba guda uku da ake zargi da aikata laifin fashi da makami a ranar Alhamism 26 ga watan Yuli, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wadanda ake tuhumar sun hada da Hassan Sanni, Babatunde Ojo da Akeem Alabi, ana tuhumarsu da tuhume tuhume guda biyu da suka hada da hadin kai, da kuma fashi.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Buhari ya sabunta lasisin mallakar rijiyoyin mai guda 25

Dansanda mai shigar da kara Michael Unah yace yan Achaban biyu sun yi amfani da rodi wajen yi ma wani abokin aikinsu Anoiteng Ikawu fashi, inda suka kwace masa babur kirar Bajaj a ranar 29 ga watan Yuni da misalin karfe 9 na dare a unguwar Elegushi.

Wata Kotu ta tasa keyar yan fashi da makami guda 3 dake fakewa da sana’ar Achaba

Sana’ar Achaba

Dansanda Unah yace yan fashin sun daidaici lokacin da Dan Achabar yake kokarin basu canjin kudin da suka bashi ne bayan ya saukesu a wurin da suka yi zai kai su, anan ne suka buga masa karfe, suka arce da babur, shi kuma ya saka kuwwa wanda hakan ya janyo hankalin jama’a suka bisu, har suka kamo su.

Bayan sauraron karar, Alkalin Kotun, A.A Fashola ya umarci a garmake masa yan fashin a kurkukun Kirikiri har lokacin da ya samu shawarar yadda za’a cigaba da shari’ar daga ofishin babban jami’I mai shigar da kara na jihar Legas, sa’annan ya dage sauraron karar zuwa ranar 5 ga watan Satumba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel