Gwamnatin jihar Legas za ta fara biyan Limamai da Malamai Albashi
Gwamnatin jihar Legas ta bullo da wani sabon shirin da zai samar da albashi da Malaman addinin Musulunci da Limaman Masallatai don su cigaba da tarbiyantar da al’ummar jihar game da ayyukan cin hanci da rashawa, inji rahoton Daily Trust.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito kwamishinan cikin gida na jihar Legas, Abdulhakeem Abdulateef ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, 26 ga watan Yuli a yayin taron wata kungiyar addinin Musulunci mai suna Al-Habibbiyah da suka gudanar da a Legas.
KU KARANTA: Hatsari ba sai a Mota ba: Mutane 5 sun gamu da ajalinsu yayin da Kwalekwale ta kifa dasu
Kwamishinan yace gwamnatin jihar ta kammala shirin aiki da wasu Malaman addinin kirista da na Musulunci da kuma Limaman Masallata wajen dabi’antar da mabiyansu mazauna jihar Legas tare da wayar musu da kai game da sharrin rashawa da kuma munanan halaye.
“Limami da Fastoci mutane ne masu matsayi a wajen Ubangiji, don haka muna bukatar ku dage wajen wayar da kawunan mabiyanku game da kyawawan dabiu, musamman a game da amana da yaki da rashawa.
“Mu tuna Allah zai tambayi dukkaninmu game da yadda muka gudanar da rayuwarmu a ranar kiyama, don haka yafi dacewa ace Malamanmu da Limamai ne zasu nuna mana hanyar tsira saboa sune shuwagabanninmu.” Inji shi.
A nasa jawabin, shugaban kungiyar, Fuad Adeyemi ya bayyana cewa kungiyar na iya bakin kokarinta wajen hada kai da Malamai domin su wayar da kan jama’a game da illolin rashin rikon amana da zalunci ta amfani da Dokokin addini.
Shima wakilin hukumar EFCC a taron, Umar Hadejia ya jinjina ma kungiyar Habibbiyah da irin gudunmuwar da suke baiwa hukumar wajen wayar da kan al’umma game da yaki da cin hanci da rashawa, sa’annan yace EFCC zata cigaba da aiki tukuru don ganin ta samu galaba akan rashawa.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng