Kasar Amurka ta yi fatali da karar da yan Biyafara suka shigar da Najeriya
Watan Kotun DC dake kasar Amurka ta yi fatali da karar da yayan kungiyar rajin kafa kasar Biyafara a Najeriya, IPOB, suka shigar da gwamnatin tarayya a gabanta, inda suka nemi gwamnati ta basu fansar miliyoyin daololi, inji rahoton Daily Trust.
Haka zalika IPOB ta bukaci kotun ta tilasta ma gwamnatin Najeriya biyanta kasha Arba’in daga cikin dala miliyan 550 kudaden da ake zargin Abacha ya sata, kamar yadda lauyansu, Godson M Nnaka ya bayyana.
KU KARANTA: Hatsari ba sai a Mota ba: Mutane 5 sun gamu da ajalinsu yayin da Kwalekwale ta kifa dasu
Majiyar Legit.ng ta ruwaito bayan da gwamnatin tarayya, IPOB ta shigar da karar babban hafsan Sojan kasa, Tukur Buratai, shugaban hukumar DSS, Lawal Daura, tsohon shugaban Yansandan Najeriya, Solomon Arase da magajinsa, Ibrahim Idris, sai gwamnonin Abia da Anambra, Okezie Ikpeazu da Willie Obiano.
Karar da suka shigar kuwa ya danganci tauye musu hakkoki da suke zargin gwamnatin Najeriya da sauran wadanda ta shigar kara suka yi musu, kuntata ma yayan kungiyar da kuma yi musu kisan gilla a tsakanin shekarar 2016 da 2017.
Alkali mai sharia Dabney Friedrich ya bayyana karar da IPOB ta shigar bas hi da inganci, sakamakon bashi da hurumin kama jami’an gwamnatin Najeriya saboda suna da kariya a kasashen waje, don haka IPOB basu da hurumin shigar dasu kara tun a farko, hakan ya sa yayi watsi da karar gaba daya.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng